Julian Assange ya gurfana a Kotun Birtaniya | Labarai | DW | 11.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Julian Assange ya gurfana a Kotun Birtaniya

Jagoran shafin WikiLeaks Julian Assange ya shiga hannun hukuma ne bayan da kasar Ecuador ta soke izinin bashi mafaka a birnin London.

Jakadan kasar Ecuador ne ya umarci 'yan sanda su kama mutumin da ya kirkiro shafin WikiLeaks bisa zargin karya ka'idojin mafaka da kasar ta bashi a ofishin jakadancinta da ke Birtaniya.

Julian Assange mai shekaru 47 ya samu izinin mafaka a ofishin jakadancin kasar Ecuador tun shekarar 2012 wato shekaru bakwai kenan da nufin kaucewa hukuncin zargin fyade da kasar Sweden ke masa. Ko da ya ke Sweden din ta soke binciken da take masa. A yanzu dai Julian Assange yana fuskantar shari'a a Birtaniya.