Juba ta fara shari′ar wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 14.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Juba ta fara shari'ar wadanda ake zargi da yunkurin juyin mulki

Wannan shari'ar na zuwa ne yayin da har yanzu ba a cimma matsaya ba a tattaunawar gano bakin warware rikicin Sudan ta Kudu da ya yi sanadiyar rayukan dubban mutane.

Bari mu fara da jaridar Neue Zürcher Zeitung wadda a wannan mako ta mayar da hankali a kan shari'ar da aka fara yi wa mutanen da ake zargi da yunkurin juyin mulki a Sudan ta Kudu.

Ta ce a ranar Talata a birnin Juba aka fara zaman sauraron shari'ar manyan 'yan siyasa hudu da shugaba Salva Kiir ya zarga da hada baki da tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa. Ana kuma zargin mutanen da suka hada da tsohon babban sakataren jam'iyyar SPLM da tsoffin ministocin harkokin waje da kuma na tsaro da laifin yada labaran karkaya da kuma haddasa rigingimu. Mutanen hudu dai na daga cikin 11 da a watan Disamban bara aka kama bisa yunkurin juyin mulkin. Sai dai a watan Janeru shugaba Kiir ya saki bakwai daga cikinsu wadanda kuma ya ba su damar zuwa Kenya. Hakan dai na zuwa ne yayin da har yanzu aka kasa cimma wata matsaya a tattaunawar warware rikicin kasar da ya yi sanadiyar rayukan mutane kimanin 10000, tun bayan barkewarsa a tsakiyar watan Disamba.

Koma baya ga matan da aka yi wa shayi

Har yanzu dai muna kan jaridar ta Neue Zürcher Zeitung wadda ta labarto wani cece-kuce lokacin bikin bude wani asibiti a kasar Burkina Faso.

A ranar Asabar ta makon da ya gabata aka shirya gudanar da bikin bude wani asibitin farko na yi wa matar da aka wa kaciya tiyata don kwaskware wannan shayin da aka yi musu, amma gwamnati ta ki amincewa da bude asibitin sa'o'i kalilan kafin a kaddamar da asibitin da ke garin Bobo Dioulasso. To sai dai duk da haka an yi wa wasu matan tiyata. Kafofin yada labaru sun ce ministan kiwon lafiya na kasar ta Burkina Faso ya ba da hujjar wannan mataki da aka dauka da rashin izinin gina asibitin. Sai dai kungiyar Clitoraid da za ta kula da asibitin ta ce ma'aikatar kiwon lafiyar ta yi suka kasancewa wata kungiyar Kiristocin darikar Raelian masu akidar garwaya karantarwa littafin Bible da wasu abubuwa na kimiyyar badini, ke ba da kudin tafiyar da aikin. Da yawa daga cikin likitocin dai mabiya wannan darika ne. Wasu rahotannin kuma sun ce gwamnati ta dauki matakin ne bisa matsin lamba daga cocin Katholika, wadda ke adawa da darikar ta Raelian.

Inshorar lafiya ta farko mafi inganci a Afirka

Ita kuwa jaridar General-Anzeiger tsokaci ta yi a kan abin da ta kira nasara ga nahiyar Afirka sannan sai ta ci gaba kamar haka.

Tare da taimakon Jamus an samar da wani tsarin inshorar lafiya da ya kunshi dukkan 'yan kasar Ruwanda. Yanzu haka kimanin kashi 91 cikin 100 na ilahirin 'yan kasar ta Ruwanda ke cin gajiyar wannan tsarin inshorar lafiya da ke zama irinsa na farko a nahiyar Afirka. Kungiyar hadin kan taimakon raya kasa ta Jamus wato GIZ ta ba da gagarumar gudunmawa wajen cimma wannan kyakkyawan matsayin na kiwon lafiya a kasar ta Ruwanda. Tun da jimawa dai samar da kyakkyawan tsarin kiwon lafiya na zaman babban aikin da kungiyar ta GIZ ta saka a gaba. Sai dai duk da wannan ci gaban wata matsala a kasar shi ne karancin likitoci da ma'aikatan kiwon lafiya sai kuma uwa-uba karancin kudi, abin da ya sa ake saka ayar tambaya game da dorewar wannan tsarin inshorar kiwon lafiyar.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Zainab Mohammed Abubakar