1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jonathan ya umurci yin bincken kisan farar hula a Baga

April 23, 2013

A wani abun dake zaman ba sabun ba gwmantin Tarrayar Nijeriya tace zata yi bincike kan kisan mutane kusan dari biyu a garin Baga dake jihar Borno a karshen mako bayan fushi daga sassa dabam dabam na kasar

https://p.dw.com/p/18LT8
Hoto: picture alliance/AP Photo

A wani abun dake zaman ba sabun ba gwmantin Tarrayar Nijeriya tace zata yi bincike kan kisan mutane kusan dari biyu a garin Baga dake jihar Borno a karshen mako. Sannu a hankali dai kura tana kara lafawa sannu a hankali kuma girman barnar yana kara fitowa fili a idon mahukuntan Tarrayar Najeriya da ke shirin kaddamar da wani kwamitin neman sulhunta tsakanin ta da yayan kungiyar boko haram mai fafutuka da boma bomai.

A karo na farko dai gwamantin da ta share tsawon lokaci tana bada kariya ga aiyyukan jamian tsaron ta dake yakin dai ta fito tace zata bincika da nufin gano ko an wuce gona da iri a cikin harin da ya hallaka mutane kusan dari biyu ya kuma dora ayar tambaya ga sabon shirin afuwar. Fadar a wata sanarwar da ta fitar cikin daren jiya dai tace bata da burin daukar ran yan kasar da basu jiba ba su gani ba, sannan kuma bata da burin kyale soja dama ragowar jamian tsaro wuce ka'idar aikin da hukumomin tsaron kasar suka shimfida musu.

Sabon matsayin dake zaman ba sabun ba dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da maida martani mai daci a ciki da wajen kasar ta Najeriya kan harin dake zaman mafi girma tun bayan barkewar rikicin shekaru sama da ukun da suka gabata. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu babu tabbacin da dama daga cikin yan kwamitin na mutane 26 da gwamantin ta kara yawansu da mace ta farko da nadin Aisha Wakil dake zaman wata lauya mai zaman kanta zasu kai ga amincewa cikin shirin gwmantin dai daga dukkan alamu, akwai hasashen kara fuskantar jan aiki a bangaren yan kwamitin da aka dorawa alhakin shiga lunguna da skunan kasar da nufin ganawa da yayan kungiyar. Mallam Garba Umar Kari dai na zaman masani na harkokin zamantakewa a jamiyar babban birnin tarraya ta abuja, kuma a cewar sa babban kuskure ne a bangaren gwamantin na kyale kai shi kansa harin tun da farko.

Sicherheitstreffen Nigeria
Manyan jami'an tsaron NajeriyaHoto: DW

Tuni dai martani ya fara fitowa daga sassa na duniya da suka hada da kasar Amurka da ta nemi mahukuntan na Abuja da su biya dukkanin hallatattun bukatun al'umar arewacin kasar ta Najeriyar a wani abun dake zaman alamu na kara kware baya ga Abujar dake fatar samun kawa a cikin yakin na ta'addanci.

Su kansu shugabannin al'ummar ta jihar Borno dai sun fara gargadin tura-ta-kai-bango, kuma hakurin su ya kare wa gwamantin da ta sha nadin kwamitoci kan rikicin amma kuma tana kin amfani da rahotannin nasu abun da kuma a cewar Senata Ahmed Zanna dake zaman dan majalisar dattawan kasar daga Borno ke iya jawo matsala babba.

Goodluck Jonathan
Shugaban Najeriya Goodluck JonathanHoto: picture alliance / dpa

Abun jira a gani dai na zaman nasarar kwamitin da zai karya kumallo a g safiyar gobe zai kuma bude sabon babi a cikin rikicin.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu