John Kerry zai fara yin ziyarar aiki a Turai | Labarai | DW | 13.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

John Kerry zai fara yin ziyarar aiki a Turai

Munufar ziyarar shi ne tattauna batun yakin Siriya da na Ukraine da kuma wasu sauran rigingimu da ake fama da su.

Sakataran harkokin wajen Amirka John Kerry zai fara yin wata ziyara aiki a cikin kasashen Rasha da Faransa da kuma Birtaniya domin tattauna batun yaki Siriya da kuma wasu rigingimu.Da farko Kerry zai yadda zango a birin Paris na Faransa,kafin ya isa a birnin Moscow na Rasha inda zai gana da shugaba Vladmir Putine,wanda tare za su tattauna batun yakin Siriya da Ukraine da kuma rikicin da ake yi a Armenia da Arzarbaidjan.