John Kerry na tattauna batun tsagaita wuta a Yemen | Labarai | DW | 07.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

John Kerry na tattauna batun tsagaita wuta a Yemen

Sakataran harkokin wajen Amirka john Kerry ya isa a birin Riyad na Saudiyya.

A ziyarar shugaban zai tattauna da shugabannin a kan batun tsagaita buɗe wuta na wani ɗan lokaci,domin isar da kayan agaji da kuma ba da dama ga wasu dubban jama'ar da su ficce daga ƙasar.

Kerry wanda ya taso daga Djibouti an shirya zai gana da sarki Salmane da kuma shugaban ƙasar ta Yemen mai yin gudun hijira Abdu Rabo Mansur Hadi.