John Fru Ndi dan siyasa ne na kasar Kamaru, wanda ya kafa babbar jam'iyyar adawa ta SDF (Social Democratic Front) a harshen Ingilishi ko (Front Social-Démocratique) a Faransanci.
Ya kasance daya daga cikin wadanda suka yi fafutuka don ganin Kamaru ta rungumi tsarin demokaradiyya. Sannan ya tsaya takarar shugabancin kasa so da dama. John Fru Ndi ne ma madugun 'yan adawa a wannan kasa.