1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon mataimakin Obama zai tsaya takarar shugaban kasa

Ramatu Garba Baba
April 25, 2019

Joe Biden, tsohon mataimakin shugaban kasar Amirka ya baiyana anniyarsa ta tsaya wa takarar shugabancin kasar a zaben da za a yi a 2020.

https://p.dw.com/p/3HRjm
USA, New York: Joe Biden
Hoto: picture-alliance/AP/F. Franklin

Biden da ya kasance mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin Barack Obama a inuwar jam'iyyar Demokrat, ya kasance dan siyasa mai farin jini a tsakanin 'yan takara ashirin na jam'iyyar ta Demokrat da suka shiga wannan takara.

A yayin wannan sanarwa ya soma da soki Shugaba Donald Trump kan kalaman da ya furta a lokacin wani rikici mai nasaba da wariyar launin fata da ya auku a jahar Virginia a Satumbar 2016, kan kisan wani bakar fata da aka zargi 'yan dan sanda da laifin yi.

Kalaman da Biden ya ce mai hadari ne da bai taba jin irinsa ba daga bakin wani shugaba a tsawon rayuwarsa, ya ce dole a dakatar da Trump daga ci gaba da mulki don ceto kasar daga bala'i da kalaman wariya za su iya janyowa. Dan shekaru saba'in da shida da haihuwa, zai kasance shugaban kasa mafi yawan shekaru in har da ya taba dare mulki in har ya yi nasara a zaben.