Jirgin yakin Taiwan ya yi batan dabo
November 8, 2017Talla
Rundunar sojin kasar ta Taiwan ta ce da misalin karfe 10 da mintoci 43 agogon GMT ne wato mintoci 34 bayan tashin jirgin yakin na Mirage 2000 da matukinsa Ho Tzu-yu na'urar hangen jirgi ta daina ganinsa. Mahukuntan kasar ta Taiwan sun sanar da tanadin wasu jiragen sama 17 da na ruwa 10 na yaki domin cigiyar jirgin. A shekara ta 1992 ne dai kasar Taiwan ta yi odar jiragen yakin samfarin Mirage kirar Faransa guda 60. A shekara ta 2012 ma dai kasar ta taiwan ta dakatar da aiki da jiragen na Mirage a cikin wani gajeran wa'adi bayan da daya daga cikinsu ya rikito a kasar faransa tare da halaka matukinsa.