Jirgin saman sojojin Amirka ya yi hadari | Labarai | DW | 11.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin saman sojojin Amirka ya yi hadari

Wani jirgin sama na sojojin Amirka mai dauke da dakarun kasar 16 ya yi hadari a jihar Mississippi da ke kudancin kasar kuma babu wanda ya tsira da ransa daga cikin mutanen 16 da ke cikin jirgin.

Kafofin yada labaran kasar ta Amirka ne dai suka rawaito wannan labari kuma rundunar sojojin ruwan Amirka ita ma ta tabbatar da wannan labari inda ta ce wani jirginta na sama sanfarin KC-130 ya samu hadari amma ba tare da wani karin bayani ba.

Fred Randle babban daraktan kula da hadaruka na yankin ya tabbatar cewa dukannin wadanda suka mutu cikin jirgin sojojin musamman ne na Amirka. Hadarin dai ya afku ne wajejen karfe hudu na yammaci agogon Amirka wato karfe tara na dare agogon GMT, kuma ma'aikatan kashe gobara sun isa wurin domin kashe wutar da ta tashi bayan da jirgin ya fadi a wata gonar noman Ridi.

Ta shafinsa na Facbook, gwamnan jihar ta Mississippi Phil Bryant ya yi kira da a yi addu'o'i ga mamatan tare da isar da jinjinarsa ga sojojin kasar maza da mata da ke ayyukan tsaron Amirka.