Jirgin saman Laos ya fadi | Labarai | DW | 17.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin saman Laos ya fadi

Jirgin saman soji dauke da manyan jami'an gwamnatin kasar Laos ya yi hadari

Jami'ai sun tabbatar da cewa jirgin saman soji mallakin kasra Laos, dauke da manyan jama'an gwamnati ya yi hadari cikin yankin arewacin kasar, amma babu karin bayani kan abin da ya samu mutanen da ke cikin jirgin.

Kimanin mutanen 20 da suke cikin jirgin lokacin da ya yi hadari sun hada da ministan tsaron kasar Douangchay Phichit da gwamnan wani lardi na cikin wadanda suka mutu, kusan duk mutanen da ke ciki jirgin sun hallaka, amma masu aikin ceto sun gano mutane uku darai. Ma'aikatar harkokin wajen Thailand, wadda ke makwabtaka da karamar kasar ta Laos ta tabbatar da faruwar lamarin na wannan Asabar.

Mawallafi: Suleiman babayo
Edita: Zainab Mohammed Abubakar