Jirgin sama na Bangladesh ya yi hadari | Labarai | DW | 12.03.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama na Bangladesh ya yi hadari

Mutane akalla guda 40 suka mutu kana wasu 23 suka jikkata bayan da wani jirgin sama mallakar kamfanin sufurin jiragen sama na US Bangla Airlines ya fadi a kusa da birnin Kathmandu na Nepal.

Jirgin wanda ke dauke da fasinja 71 wanda ya taso daga birnin Dacca ya fadi kafin ya isa a filin saukar jiragen sama na Kathmandu. Wani wanda ya shaida lamarin ya ce ya ga lokacin da jirgin ya fadi, ya ce farko sun ga hayaki ya turnike sama kafin da baya su ji wani kara.