Jirgin sama kasar Bama ya bace da fasinjoji 116 | Labarai | DW | 07.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin sama kasar Bama ya bace da fasinjoji 116

Wani jirgin sama na sojin kasar Bama dauke da fasinjoji 116 ya yi kasa ko bisa a yankin Dawei na Kudu maso Gabashin kasar dake kusa da gabar Tekun Andaman.

Wani jirgin sama na sojin kasar Bama dauke da fasinjoji 116 ya yi kasa ko bisa a yankin Dawei na Kudu maso Gabashin kasar da ke kusa da gabar Tekun Andaman. Shugaban hafsan sojan kasar ta Bama Min Aung Hlaing ne ya sanar da hakan a saman shafinsa na Facebook, inda ya ce kusan ba zato ba tsammani jirgin ya bace daga kan na'urar hangen tafiyar jirgi. 

Jirgin dai ya taso ne tun da sanyin safiyar wannan Laraba daga birnin Myeik na kudancin kasar zuwa Rangoun babban birnin kasuwanci na kasar lokacin da ya yi kasa ko bisa. 

Mahukuntan sojin kasar ta Bama sun ce sun aika da jiragen sama da na ruwa na sojin kasar wajen aikin bincike inda tuni kuma suka gano wasu tarkace masu kama da na jirgin a teku a wani wuri mai nisan kilomita 218 da birnin na Dawei.