Bala'i
Hadarin jirgin sama a Indonusiya
October 29, 2018Talla
Kakakin kamfanin na Lion Air ya bayyana cewa jim kadan bayan tashin jirgin wanda ya kama hanyar zuwa birnin Panhkal Pinang na tsibirin Bangka, ya sanar da jami'an filin jirgin saman birnin na Jakarta bukatar juyowa, amma kuma daga bisani sai sadarwa ta tsinke tsakanin jirgin da filin jirgin saman da misalin karfe shida da rabi wato karfe 11 da rabi na dare agogon JMT.
Yanzu haka dai jami'an ceto na kasar ta Indonusiya na can na kokarin kai agaji a inda jirgin samfurin Boeing 737 ya fada ruwa a wani waje mai zurfin mita 30 zuwa 40 a cewar ofishin ministan sufurin jiragen sama na kasar.