Jirgin kasa ya kashe mutane 33 a Kwango | Labarai | DW | 13.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin kasa ya kashe mutane 33 a Kwango

Hukumomin kula da sufurin jiragen kasa sun ce mutane da dama sun jikkata a yayin da jirgin ya kife a rami, jami'ai na zargin mutanen da suka kone kurmus da shiga jirgin ba tare da izini ba.

Jirgin kasan ya fada wani rami ne a yayin da yake kokarin haura wani tudu a kan titin birnin Lubumbashi birnin na biyu mafi girma a kasar zuwa Luenana, inda jirgin ya dauko tankokin mai 13da suka fashe suka haddasa gobara nan take bayan subuce wa zuwa rami.

A baya ansha samun hatsarin jiragen kasa a yankin Luena, kungiyar agaji ta kasa da kasa Red Cross tace akalla mutane mutane sama da dari sun mutu yayin da wasu sama da mutane 160 suka jikkata a wani hatsarin jirgin kasa da ya kife a shekarar 2014.