Jirgin Boeing Dreamliner ya koma aiki | Labarai | DW | 27.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin Boeing Dreamliner ya koma aiki

Kamfanin Ethiopian Airlines, ya jarraba tashin Dreamliner, bayan matsalolin da aka gano cikin kira jirgin a baya.

An Ethiopian Airlines' 787 Dreamliner prepares for departure from the Bole International Airport in Ethiopia’s capital Addis Ababa, April 27, 2013. Ethiopian Airlines on Saturday became the world's first carrier to resume flying Boeing Co's 787 Dreamliner passenger jets, landing the first commercial flight since the global fleet was grounded three months ago following incidents of overheating in the batteries providing auxiliary power. REUTERS/Tiksa Negeri (ETHIOPIA - Tags: TRANSPORT BUSINESS)

Boeing 787 Ethiopian Airlines

Karon farko,bayan watani uku, a wannan Asabar kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Ethiopian Airlines, ya jaraba tashin jirgin Dreamliner, mallakar kamfanin Boeing na kasar Amirka.

Ranar 16 ga watan Janairun shekara bana, Hukumar dake kula da zirga-zirga jiragen sama ta Amirka, ta hana tashin jirage samfarin Dreamliner, dalili da matsalar zafin batur da aka gano.

A duk Afirka kasar Ethiopiya kadai ta mallaki wannan jirgi na zamani.

Kamafanin Ethiopian Airlines ta jaraba daya daga jiragen Dreamliner uku da ya mallaka, wanda ya tashi daga birnin Adis Ababa zuwa Nairobin kasar Kenya.

Shima kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Japan, wato All Nippon Airways zai jaraba tashin Dreamliner ranar Lahadi.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Usman Shehu Usman