Jirgin Air Asia ya bace dauke da mutane 162 | Labarai | DW | 28.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirgin Air Asia ya bace dauke da mutane 162

Hukumomin suhuri na kasar Indonesiya, sun sanar da bacewar wani jirgin kamfanin Malaisiya na Air Asia tsakanin Indonesiya da Singapore dauke da mutane 162

Da ya ke magana wa kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, kakakin ofisin ministan suhurin kasar ta Indonesiya ya ce an daina jin duriyar wannan jirgi ne na Air Asiya tsakanin Surabaya da Singapour da musalin karfe bakoye da minti 55 agogon wannan kasa. Jirgin da ya tashi daga filin jirgin sama na Juanda da ke birnin Surabaya a tsibirin Java da ke kasar ta Indonesiya da musalin karfe biya da minti 20 agogon wannan yanki, kuma ya kyautu ya sauka a filin jirgin saman Changi da ke kasar Singapour da musalin karfe takwas da minti 30, karfe 12 da rabi na dare agogon GMT, ya na dauke ne da ma'aikatan jirgin mutun bakoye da kuma fasinjoji mutun 155, cikin su yara kanana 16 da jariri guda.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Umaru Aliyu