Jiran sakamakon zaɓen kundin tsarin mulki a Masar
December 23, 2012Jam'iyun adawa a Masar, sun yi wasti da sakamakon zaɓen raba gardama game da saban kundin tsarin mulki da aka kammalla jiya.A hukunce a wannan Litinin ake sa ran baiyana sakamakon zaɓen,to saidai 'yan uwa musulmi tare da sauran ƙungiyoyin dake goya musu baya, sun ce sun samu gagaramin rijnaye tare da kashi 64 cikin ɗari na mutanen da suka amince da kundin.
'yan adawar sun ce, za su shigar da ƙara kotu domin ƙalubalantar wannan sakamako, da su kace ya na cike da maguɗi.Masu adawa da saban kundin na zargin shugaba Mohammad Mursi da ƙadamar da shari'ar musulunci a cikinsa, da kuma tauye 'yancin jama'a.
A yayin da yake tsokaci game da zaɓen na Masar ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle yayi kira ga hukumomin Alƙahira su kasance masu adalci a duk cikin al'amura.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu