Jiran naɗa shugaban gwamnatin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 14.01.2013
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jiran naɗa shugaban gwamnatin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya

'Yan adawar Jamhuriya Afirka ta Tsakiya sun miƙa sunan Nicolas Tiange a matsayin Firaminista

Har ya zuwa daren jiya Lahadi,al'ummar ƙasar Afirka ta Tsakiya na zaman jiron sanin sunan mutumen da zai ja ragamar sabuwar gwamnatin haɗin kan ƙasar da a ka yi na'am da shi bayan da aka cimma wata yarjejeniya a tattanawar da ake yi da 'yan tawayen ƙasar. Tuni dai 'yan adawa suka baiwa shugaba Bozize sunan Nicolas Tiangaye a matsayin sabon shugaban gwamnatin,to saidai a ɓangaren gwamnati,wani mai magana da yayun shugaba Bozize ya ce kawo yanzu ba su samu wata takaradar da ke nuna hakan ba. Ko daya ke ya ce har in sun bada sunan wani to kuma babu shakka shugaban ƙasar zai yi aiki da shi don gudun kada a zarge shi da ƙin cika sharuɗan yarjejeniyar. Idan dai har ta tabbata mista Nicolas na da jan aiki a gabansa ta yadda zai haɗa majalisar ministocinsa ba tare da wani shan kai ba.

Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Yahouza Sadissou Madobi

 • Kwanan wata 14.01.2013
 • Muhimman kalmomi ZAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17JM3
 • Kwanan wata 14.01.2013
 • Muhimman kalmomi ZAR
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/17JM3