Jirage za su fara aiki a tsbirin Bali | Labarai | DW | 30.11.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jirage za su fara aiki a tsbirin Bali

A kasar Indunisiya jiragen yawon bude ido na kasa da kasa za su fara zirga-zirga da dubban masu yawon bude ido bayan rufe tashar jiragen na tsawon kwanaki uku sakamakon aman wutar da duwatsun da ke yankin suka yi.

An samu sauyin shekar iska da ya rage tudun toka da hayaki a filin jirgin, aman wutar duwatsun Agung ya haifar da tarin toka da ke zama barana ga lafiyar jiragen sama wanda ya yi sanadiyar cunkushe masu yawon bude ido akalla dubu 120 tun bayan faruwar al'amarin a ranar Litinin.

A shekarar 1963 an samu aman wuta a yankin na Bali mai keweye da tsaunuka wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu daya. Duk dai da cewa a wannan karon babu asarar rai, mazauna yankin Bali sun kauracewa gidajensu don gudun sake fashewar duwatsu.