Jihar Jigawa ta gano dimbin ma′aikatan boge | Siyasa | DW | 02.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jihar Jigawa ta gano dimbin ma'aikatan boge

Bayan tankade da rairaya , jihar Jigawa tace ta binciko dubban mutanen dake kiran kansu ma'aikatan gwamnati wadanda ba ma'aikata bane a zahiri.

Yayain da ma'aikata a Nageriyar ke ikirarin a kara musu albashi,wasu jihohin kasar na fama da dubban ma'aikatan bogi. Jihara Jigawa da ke arewacin Najeriyar na daya daga cikin jihohin da ke fuskantar wannan matsalar inda jimlar yawan mutanen da ke cikinn jihar bai wuce miliyan hudu ba. Jihar jigawa dake arewacin tarayyar kasar tana da yawan mutane sama da miliyan hudu cikin su ma aikata dubu sittin da biyar. Wanban Dutse, Mustapha Aminu shine shugaban maaikata na jihar cewa yayai:

Sun gaji maikata sama da dubu saba'in da biyar amma daga baya suka tantace dubu goma ma'aikatan bogi ne. Kowace hanya suka bi ta tantacewa? Yayi karin haske akan cewa saida sukayi biyan albashi na karbi da hannunka wato[ pay parade} na tsahon wata shida. A wancan lokacin sai da suka gano cewa hatta dan da yake goye yana da albashi, kuma kari bisa wannan, sai su kama mutum guda da takardar "offer" ta daukar aiki kamar goma.

Da hadin gwiwar kungiyoyi irin su UNICEF, DFID da EU suka sami nasarar dora adadin ma'aikatan su bisa na'ura mai kwakwalwa inda aka fara biyan albashi na "e-pay ment", irinsa na farko a Najeriya. Hakan tasa sukayi rarar kudi na sama da Naira miliyan dubu bakwai. Yusuf Magaji Jigawa yayi bayani akan yadda aiki yake a da da kuma yanzu, inda banbacin da yawa, musamman ta wajen karbar albashi akan kari.

Ahmad Rabiu Vorsitzender der Industrie- und Handelskammer der nördlichen Bundesstaaten Nigeria

Ahmad Rabiu shugaban kungiyar yan kasuwa da masu masana'antu ta arewacin Najeriya

A yanzu haka jihar tana fama da samari da suka kammala karatu babu aikin yi. Magaji Iliyasu ya bayyaan takaicinsa da ake daukar ma aikatan kwantaragi maimaikon idan mutun yayi ritaya ya bari wasu masu sabon jini su sami damar maye gurbinsa. Wannan yake hana matasa samun aiki a jihar. Wani matashi da ya dade da kammala karatunsa na Diploma yace su gaskiya ba'a basu horo na sana'a ba. Karatu aka koya musu, kuma sunyi karatun ba aikin yi.

Shugaban ma aikatan yaci alwashin hukunta kowa da aka samu da laifi ba tare da sani ko sabo ba.

Mawallafiya: Zainab Shu'aibu Rabo
Edita Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin