Jerin gwanon adawa da gwamnatin Thailand | Labarai | DW | 14.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jerin gwanon adawa da gwamnatin Thailand

Masu boren adawa da gwamnatin Thailand sun sha alwashin gurgunta harkokin mulki a kasar.

Dubun dubatan masu zanga zanga ne suka yi jerin gwano a wasu ofisoshin gwamnati da ke Bangkok, babban birnin kasar Thailand. Masu zanga zangar sun fara zaman dishan a wasu muhimman wurare da kuma katse harkokkin zirga zirga a manyan titunan birnin - a wannan Litinin (13.01.14) domin cimma manufar da suka sanya a gaba ta katse harkokin yau da kullum a birnin - mai yawan mutane miliyan 12.

Hakanan masu zanga zangar sun sha alwashin ci gaba da boren nasu - har sai gwamnatin fira ministar kasar Yingluck Shinawatra's ta yi murabus, domin bada damar samar da wata majalisar 'yan kasa, amma ba ta wadanda aka zaba ba, da za ta tafiyar da harkokin kasar. Masu boren suka ce majalisar za ta aiwatar da sauye sauyen da ke da nufin yaki da cin hanci da rashawa, tare da takaita irin karfin fada a ji da kudi ke dashi a cikin harkokin siiyasa.

Idan har bore a kan titunan ya ci gaba dai, to, kuwa hakan zai janyo cikas ga zaben da fira ministar ta shirya gudanar wa a ranar biyu ga watan Fabrairun da ke tafe.

Dama cikin shekaru masu yawa ne Iyalan Yingluck da ke zama hamshakan masu kudi, suka mamaye harkokin siyasar kasar ta Thailand. 'Yan adawar kuma suna zargin dangin na ta da hannu dumu dumu wajen cin hanci da rashawa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu