Jean-Claude Juncker na cikin halin tsaka mai wuya | Labarai | DW | 10.07.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jean-Claude Juncker na cikin halin tsaka mai wuya

Fira ministan na Luzambak na daf da fuskantar wata ƙuri'a ta 'yan majalisun dokoki da ka iya tsige shi daga shugaban gwamnatin.

Jean -Claude Juncker wanda ke riƙe da matsayin na fira minista na wata 'yar ƙaramar ƙasar da ke cikin ƙungiyar tarrayar Turai ya riƙa yin juɓi, a lokacin da 'yan majalisun dokokin suke yi masa tambayoyi.

Saboda kasawa da gwamnatinsa ta nuna wajan kula da harkokin tsaro ta hanyar tattara bayanan sirri. Juncker wanda ke cikin harkokin mulkin kusan shekaru 30, masu yin  adawa da shi na zargin shi da mayar da hankali a kan ƙungiyar tarrayar Turai fiye da ƙasarsa. Kuma a kwai alamun cewar idan har aka sauke shi daga muƙamin, to kam za a iya shirya wani sabon zaɓe na kafin wa'adi a cikin watan Oktoban da ke tafe.

Mawallafi  : Abdourahamane Hassane
Edita   : Saleh Umar Saleh