Jawabin Trump na farko ga majalisa | Siyasa | DW | 31.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jawabin Trump na farko ga majalisa

Muhimman batutuwa a jawabin shugaban Amirka Donald Trump na farko a gaban zaman hadin guiwa na majalisun dokokin kasar ya na dauke da irin jawabansa a lokacin yakin neman zabensa.

USA Donald Trump Rede zur Lage der Nation

Shugaban Amirka Donald Trump

Acewar Michael Knigge na tashar DW a cikin wannan sharhin, jawabin da shugaba Trump ya dauki lokaci yana gabatar wa 'yan majalisun na Amirka ya kauce amfani da duk kalmomin da aka san shi da amfani da su a baya,  musanman na sukar abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton ko kafaffen yada labarai, batutuwan da ya ke yawan bai wa fifiko a jawabansa na baya, maimakon hakan ya mayar da hankali ne kan batun hadin kan kasa inda ya yi kira ga 'yan majalisu da su tashi tare da yi wa Amirkawa hidima. Sai dai can a tsakiyar yin jawabin ya koma kan barazanar da kasarsa ke fuskanta daga baki 'yan gudun hijra da ke zaune a kasar wasu ma ba bisa ka'ida ba. Ya kuma ce sun haifar da tarin illoli a rayuwar Amirkawa, kalaman da za a ce sun zo dai-dai da irin wanda ya yi a lokacin yakin neman zabensa. A wannan karon ma sai da ya ja hankulan Amirkawa kan ta'asar ayyukan ta'addanci da ya alakanta da aikin baki, inda nan ma kamar yadda ya fadi a can baya ya kumayin jaje ga wasu daga cikin iyalan da ke sauraron jawabin wadanda suka rasa 'yan uwa ko dangi a hannun wasu baragurbi wato baki da suka kutsa cikin kasar ba bisa ka'ida ba, da ke kuma zama barazana ga kwanciyar hankalin al'umma. Shugaban ya fito karara inda ya kara jaddada matakansa kan batun bai wa baki shaidar izinin zama da kuma daukar kwararan matakai wajen bai wa masu shaidar zaman damar iya shigo da sauran iyalansu da suka bari a kasashensu muddin suka cika sharudan da aka gindaya.

Michael Knigge Kommentarbild App

Michael Knigge na DW

Trump bai yi batun dimokaradiyya ba

Wani abu da ya bai wa jama'a mamaki kuwa shi ne yadda shugaban ya ambaci kasar Rasha da ake zargi da yin kutse a zaben Amirka musanman batun binciken da ake yi kan rawar da kasar ta taka a zaben da ya aza shi kan mulki sau guda, yayin da ya ambaci kasar China sau uku, amma ko sau guda bai ambanci kalmar Demokradiyya ba. A yayin da jawabin na Trump na farko kan halin da kasa ke ciki ya sami karbuwa a tsakanin 'yan siyasa da kuma daga martabar jam'iyyarsa ta "Republican'' za a iya cewaya yi amfani da jawabin nasa wajen yin kira ga 'yan jam'iyar tasa da ma na jam'iyyar adawa ta Democrats da su kare dukkan 'yan kasa ba tare da nuna banbanci ba. Duk da haka jawabin ya yi tasiri, ta yi wu ya kawo karshen cece-kuce na cewa Donald Trump shugaba ne mai niyyar hada kan al'umma da kuma sauya salon shugabancinsa.