Jawabin shugaba Joachim Gauck | Labarai | DW | 22.02.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin shugaba Joachim Gauck

Shugaban ƙasar Jamus ya baiyana buƙatar ƙarin cuɗayya tsakanin ƙasashen EU.

Shugaban ƙasar Jamus Joachim Gauck, ya gabatar da jawabi inda ya taɓo batutuwa daban-daban da su ka jiɓancin matsalolin da ƙasashen Turai ke fuskanta, da kuma ma'amala tsakanin Jamus da maƙawftanta na Tarayya Turai.

Shugaba Gauck ya baiyana damuwa game da kariyar tattalin arzikin wasu ƙasashen Turai, to saidai ya ƙara da cewa babbar matsala itace ƙarancin taimakon juna, da kuma rashin yarda da fara shiga tsakanin ƙasashen EU.

A ɗaya wajen, ya maida martani ga masu zargin Jamus da yin shishigi cikin harkokin ƙasashenTurai:

Yace:Ina mamaki yadda wasu ke yi mummunar fasara ga rawar da Jamus ke takawa a Tarayya Turai.Ba mu da burin shimfaɗa mulkin kama karya, saɓanin yadda wasu ke zargin mu.

Buƙatarmu kawai,itace samar da cigaba a ko wace ta hanyar matakan yaƙi da almubazaranci.

Shugaban Jamus ya yi kira ga al'umomin ƙasashen Turai su ƙara bada amana da yarda ga wannan ƙungiya, wada ke matsayin garkuwa a gare su.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Halima Balaraba Abbas