Jawabin shugaba Bashar Al-Assad | Labarai | DW | 06.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jawabin shugaba Bashar Al-Assad

Shugaban Siriya ya ce ba zai hau teburin shawara ba da " 'yan amshin shatan ƙasashen ƙetare".

Shugaba Bashar Al-Assad na Siriya ya gabatar da dogon jawabi, wanda a cikin sa ya taɓo batutuwa da dama da su ka haɗa da gwagwarmaya da wanda ya kira 'yan ta'ada.

Gaban dubunan magoya baya da ke taɓa masa, shugaba Assad ya yi kira g al'uma su ƙara ɗaura ɗamara yaƙi ,domin yaƙar 'yan tawaye da ya dangata da 'yan amshin shatar ƙasashen ƙetare.

"Muna da shaidu cikkaku na cewar da dama daga masu kiran su mazajen juyin juya hali, membobin Alqa'ida ne"

Saidai a ɗaya hannun, Assad ya ce a shirye ya ke ya tattauna da ƙungiyoyin tawayen dake buƙata, bayan yaƙi ya ƙare,amma banda masu karɓar umurni daga waje.

Sannan a shirye ya ke ya girka gwamnatin haɗin kan kasa, amma ta hanyar yin amfani da dokokin da ƙasa su ka tanada.

Shugaban Siriya ya isar da godiya ta mussamman ga ƙasashe Rasha, China da Iran ,wanda suka ba shi haɗin kai a cikin wannan gwagwarmaya.

Kusan shekaru biyu kenan da Siriya ta faɗa cikin mummuman rikic

Tuni ƙasashen duniya sun fara maida martani ga wannan jawabi.Kungiyar EU ta ce sam ba za ta wiwu ba a girka gwamnatin riƙwan ƙwarya tare da Assad, a yayin da shi kuma ministan harkokin wajen Birtaniya ya dangata jawabin da rashin imani

Yaƙin Siriya kawo yanzu a cewar Majalisar Dinkin Duniya ya haddasa mutuwar mutane fiye da dubu 60.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Umaru Aliyu