Shugaba Barack Obama ya yi jawabinsa na karshe a matsayin shugaban kasa ga al'ummar Amirka a birinin Chicago inda sama da mutane dubu 20 suka taru don yin ban kwana ga shugaban.
Shugaban na Amirka ya ambato irin nasarorin da ya samu a tsawon shekaru takwas na mulkinsa,game da batun yrjejeniyar da ya cimma da Iran da batun inshora na kiwon lafiya da kuma halarta auren jinsi a Amirka.sannan kuma ya ambato batun wariyar launin fata da ta'addancin wadanda ya ce suna zaman barazana ga demokaradiyya.Shugaban dai ya rika yin hawaye a lokacin da ya ambato irin gudunmowar da maidakinsa ta kawo masa wajen yin mulki.