1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikicin yankin Tigray da rashin tabbas a Afirka ta Tsakiya

Zainab Mohammed Abubakar MNA
December 2, 2022

Rawar da Iritiriya ke takawa arikicin Tigray na kasar Habasha da wani hari da jirgin saman yaki ya kai a Jamuriyar Afirka ta Tsakiya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/4KPd7
Nairobi Kenya | Yarjejeniya tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan Tigray | Birhanu Jula da Tadesse Werede Tesfay
Birhanu Jula da Tadesse Werede Tesfay bayan rattaba hannu kan yarjejeniya tsakanin gwamnatin Habasha da mayakan Tigray a birnin Nairobi, KenyaHoto: Thomas Mukoya/REUTERS

Za mu fara ne da labarin da jaridar Neue Zürcher Zeitung ta wallafa mai taken "Shin Iritiriya na zagon kasa dangane da zaman lafiya a Tigray? Makwabciyar kasar ta taka rawar gani sosai a yakin basasar kasar Habasha".

Jaridar ta ci gaba da cewar, bangarorin da ke gaba da juna a kasar Habasha sun rattaba hannu kan takardu biyu a watan da ya gabata, da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma shirin aiwatar da shi. Tare da fatan cewa nan ba da dadewa ba za a iya kawo karshen rikicin, wanda a halin yanzu ya fi kowanne yawan mace-mace a duniya kuma ya yi sanadin mutuwar dubban daruruwan mutane. Sai dai akwai abubuwa biyu da suka zame wa yarjejeniyar kadangaren bakin tulu, a cewar jaridar: "karfin matsi daga ketare" da "dakaru na kasashen waje."

Iritiriya mai gwamnatin kama-karya da ke a yankin kahon Afirka mai yawan jama'a kusan miliyan shida ta hada iyaka da Tigray, da ke yankin arewacin Habasha inda aka gwabza daya daga cikin munanan yake-yake tun daga watan Nuwamba 2020. Iritiriya ta tabka barna a Tigray. Dakarun Asmara sun goyi bayan sojojin Habasha, wadanda suka nemi murkushe gwamnatin tawaye na yankin. Ana zargin sojojin Iritiriya da aikata munanan laifuka a yakin da ake yi da suka hadar da kisan gilla kan fararen hula da kuma fyade ga jama'a.

Wata guda bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta, har yanzu sojojin Iritiriya na nan a yankin na Tigray duk da cewa janyewar "dakarun kasashen waje" wani sharadi ne na shirin samar da zaman lafiya mai dorewa.

Yarjejeniyar tsagaita bude wuta da wakilan Tigray da gwamnatin Habasha suka sanya wa hannu a ranar 2 ga watan Nuwamba a Pretoria babban birnin kasar Afirka ta Kudu, ya biyo bayan kazamin fadan da aka kwashe makonni ana gwabzawa a yankin na Tigray. A karshen watan Agusta, fada ya sake barkewa bayan tsagaita bude wuta na tsawon watanni. A cikin watanni biyun da suka biyo baya, an kashe mayaka fiye da 100,000 a fagen daga, a cewar alkalumman da kungiyar nazarin rigingimu ta kasa-da-kasa.

Zentralafrikanische Republik Blaise-Didacien Kossimatchi von der Nationalen Galaxie
Zanga-zangar nuna goyon baya ga girke sojojin Rasha a Afirka ta TsakiyaHoto: CAROL VALADE/AFP via Getty Images

"Bama-bamai na fatalwa a Bossangoa" da haka ne jaridar die Tageszeitung ta bude sharhin da ta rubuta game da rahoton da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta bayar kan wani hari ta sama kan sojojin hayar Rasha da ke kawance da ita.

A cewar jaridar, an kai wani hari ta sama a garin Bossangoa da ke arewacin kasar, kamar yadda sanarwar gwamnatin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta nunar daga babban birni Bangui. A wannan yankin ne ake da sansanin sojojin kasar da kuma na kawayensu daura da wata masana'antar auduga. Bugu da kari wadannan bama-bamai sun janyo hasarar dukiya mai yawa. Jirgin da ya kai harin da ba a tantance shi ba ya bar sararin samaniyar Afirka ta Tsakiya zuwa arewa, in ji sanarwar.

Akwai yiyuwar wannan sanarwar ta mayar da rashin zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya zuwa rikicin kasa da kasa. "Kawayenta" da aka jefa wa bama-bamai dai na nufin Rasha, wacce ke da mayaka da dama daga rundunar sojojin haya ta Wagner masu zaman kansu, wadanda suka shahara da ta'addanci, da aka tura a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da kuma 1,345 "masu ba da shawara" da "masu koyarwa" tare da sojojin, a cewar alkaluman hukuma.

Makwabciyar arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ita ce kasar Chadi, babbar kawancen sojan Faransa a yankin da ke da sansanin sojin saman Faransa na dindindin a babban birnin kasar wato Njamena, inda kuma sojojin sama na Chadi suke.

Faransa da Rasha dai abokan adawa ne a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Kasar da ke fama da talauci amma mai arzikin ma'adinai ta kasance cibiyar tsoma bakin sojojin Faransa tsawon shekaru da dama. Sai dai Faransa ta janye a shekarun baya-bayan nan, yayin da shugaba Faustin-Archange Touadéra da ke kan karagar mulki tun a shekarar 2016, ya kulla alaka da Rasha, wadda ba kamar Faransa ba, ke ba da taimakon soji domin yakar 'yan tawaye, sannan kuma tana yakar su kai tsaye.

Mayakan Wagner na Rasha sun hana kifar da gwamnatin Touadéra a karshen shekarar 2020, bayan wani farmaki da ‘yan tawaye suka kai, jim kadan kafin a tabbatar da shi a kan karagar mulki, inda ya lashe kashi 54 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben da da ma ba zai iya faruwa ba saboda rashin tsaro a galibin sassan kasar.

Proteste im Sudan
Masu zanga-zangar neman dawo da gwamnatin farar hula a SudanHoto: Marwan Ali/AP Photo/picture alliance

Ita kuwa jaridar Der Tagesspiegel labari ta buga mai taken "Shin ina Sudan ta dosa" yin sulhu don neman zaman lafiya. Jaridar ta ce a ranar 25 ga Oktoba, 2021, juyin mulkin soji ya kawo karshen tsarin mika mulki ga farar hula wanda aka fara a shekarar 2019, bayan juyin juya hali da ya kawo karshen mulkin kama karya na shekaru 30 a wannan kasar.

A cikin shekaru biyu kafin juyin mulkin, gwamnatin farar hula ta wucin gadi ta yi sulhu da kungiyoyin 'yan tawaye da dama, ta kaddamar da sauye-sauye a fannin tattalin arziki da na shari'a, da kuma kyautata alaka da wasu jihohi.

Hadin gwiwar da ke tsakanin jam'iyyun farar hula da sojoji, wanda ya kamata ya saukaka mika mulki ga mulkin demukuradiyya, ya wargaje ne saboda rigingimun siyasa. Har yanzu dai sojoji ba su yi nasarar kafa gwamnati mai aiki ba saboda ci gaba da turjiya da kuma nuna adawa da juyin mulkin.

Sama da matasa 120 ne aka kashe a zanga-zangar adawa da sojoji. "Tattalin Arziki ya tsaya cak. Al'umar Sudan miliyan 15 na rayuwa cikin yanayi na barazanar rashin abinci." .Yawancin kasashe masu ba da taimako sun dakatar da taimakon raya kasa.

Ana ci gaba da bayar da agajin jin kai na kasa da kasa, amma akasarin kasashe masu ba da agaji ciki har da Jamus sun dakatar da taimakon raya kasa da suka yi alkawarin bayan juyin juya halin.