Janyewar dakarun Faransa daga Mali | Labarai | DW | 21.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Janyewar dakarun Faransa daga Mali

Faransa, wadda ke kan gaba wajen daukar matakin soji a Mali, ta ce yankunan kasar na kan hanyar sake dunkulewa wuri guda.

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana cewar cikin tsukin kwanaki kalilan masu zuwa ne yankunan kasar Mali daban daban da suka sullubewa hukumomin kasar za su koma a karkashin ikon gwamnatin. Sanarwar da mahukuntan na Paris suka fitar dai, ta zo ne bayan da a wannan Larabar, mahukunta a birnin suka ce suna kokarin tantance gaskiyar ikirarin da kungiyar alqa'ida reshen arewacin Afirka ta yi na cewar ta kashe wani ba-Faranshe da ta yi garkuwa da shi- a matsayin martani ga matakin sojin da ita Faransar a dauka a Mali.

Shugaba Hollande ya fadi a lokacin wata liyafar cin abincin dare tare da wakilan kungiyar Yahudawa mazauna Faransa cewar a yanzu matakin sojin da kasar Faransa ta dauka tare da goyon bayan wasu kasashe a Mali, yana babinsa na karshe ne. Shugaban na Faransa ya yi wannan fuirucin ne jim kadan bayan da firayiministan kasar Jean-Marc Ayrault ya ce nan da karshen watan Afrilu ne dakarun Faransa da ke Mali za su fara janyewa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mouhamadou Awal Balarabe