Jana'izar tsoron jami'in tsaron Lebonon ta rikiɗa ta zama zanga-zanga
October 21, 2012
A wannan Lahadin ce a ka yi zina'izar shugaban hukumar tsaro ta Lebonon wato janar Wissam al-Hassan wanda ya hadu da ajalinsa a wani harin tashin bom a wata mota a ranar Juma'an da ta gabata. Jim kadan bayan zina'izar ne daruruwan mutane suka yi yunkurin ktsawa a fadar gwamnatin kasar domin nuna bacin ransu ga dangantakar da ke tsaakanin jam'iyar shi'a ta Hezbollah da gwamnatin kasar.
Da dama ne daga cikin 'yan kasar ke zargin kungiyar ta Hezbollah da hannu a kisan jami'in wanda ke da alaka da tsohon pramiyan kasar Rafic Hariri wanda aka hallaka cikin wani makamancin wannan harin. Rahotani sun tabbatar da harbe harbe tsakanin jami'an tsaro da kuma masu zanga zangar to saidai babu rahotanin da ke tabbatar da mutuwar mutane.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Umar Aliyu