Jana′izar Brian Moore a kasar Amirka | Labarai | DW | 08.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jana'izar Brian Moore a kasar Amirka

Dubunnan al'ummar birnin New York sun halarci jana'izar Brian Moore wani dan sanda da wasu su ka kashe da Bindiga.

A kasar Amirka a ranar juma'a dubbunnan jama'a ne a birnin New York suka halarci jana'isar Brian Moore wani dan sanda wanda ya mutu a sakamakon raunin da ya ji bayan da wasu da ba a san ko suwane ba suka harbeshi da Bindiga a ka a ranar assabar din da ta gabata a wata unguwar Birnin na New York.Shi dai wannan dan sanda wanda matashi ne dan shekaru 25 a duniya shi ne dan sanda na ukku na birnin New York da aka kashe daga tsakiyar watan disambar da ya gabata zuwa yau.Tuni dai aka kama wani mutun bakar fata dan shekaru 35 da ake zargi da aikata kisan

Mutuwar wannan dan sanda dai ta zo ne a daidai lokacin da ake cikin wani yanayin zaman doya da man ja tsakanin bakaken fata da yan sandar kasar biyo bayan jerin wasu kishe kashen gillar na bakar fata da yan sandar kasar su ka yi wanda ya haddasa zanga-zanga dama kone-kone a wasu biranan kasar a yan watannin baya-bayannan