1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Badakalar tauye hayakin motocin Volkswagen

Abdullahi Tanko Bala
September 30, 2020

Tsohon shugaban sashen motocin Audi na kamfanin Volkswagen da wasu mutane uku sun gurfana a kotu kan magudin tauye hayakin da motocin kamfanin masu amfani da man diesel suke fitarwa.

https://p.dw.com/p/3jE98
Rupert Stadler
Hoto: Getty Images/C. Stache

Shari'ar na zama ta farko da ake dauka a matsayin babban laifi na cin amana a Jamus game da tabargazar da ta faru shekaru biyar da suka wuce wanda ya janyo wa rukunin kamfanonin Volkswagen hasarar samar da euro biliyan 32 wajen biyan tara da kuma wasu hakkoki domin yin sulhu.

Rupert Stadler da sauran mutane uku da ake zargi, ana tuhumarsu ne da zamba cikin aminci da tafka karya kan hakikanin hayakin da motocin ke fitarwa da kuma tallata motocin kan tafarkin karya.

Kotun Munich da za ta gudanar da shari'ar za ta yi zama 176 na sauraron shari'ar wadda za ta dauki tsawon lokaci zuwa watan Disambar shekarar 2022.