Jamus za ta tallafa da jiragen yaki don yakar IS | Labarai | DW | 26.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta tallafa da jiragen yaki don yakar IS

Tarayyar Jamus na shirye-shiryen bayar da gudunmowar jiragen yaki kirar Tornado gami da hada hannu da al'umomin kasashen duniya don murkushe kungiyar IS.

Yanke hukuncin aikewa da jiragen yakin hudu zuwa shidda yazo ne a dai-dai lokacin da majalisar ministocin tarayyar Jamus suka kammala wani taron sune a ranar alhamis a birnin Berlin.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta amince da hakan ne bayan tattaunawa da shugaban kasar Faransa Francois Hollade akan sake kara kaimi wajen bayar da tallafin murkushe ayyukan kungiyar Is.

Taron dai da Shugaba Angela Merkel ta kira ya hada da ministan harkokin wajen kasar Frank Walter Steinmeier,da ministar tsaro Ursula Von der leyen don duba yuwuwar irin rawar da Jamus zata taka akan batun hada hannu da karfe da Faransa don yakar Is.