Jamus za ta ba da tallafi ga Ecowas | Labarai | DW | 16.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus za ta ba da tallafi ga Ecowas

Jiragen sama masu dakon kayayaki shi ne tallafin da ƙasar za ta bayar ga ƙungiyar ƙasashen yankin yammacin Afirka saboda rikicin Mali

Auf dem Flugplatz in Kundus steht diese Transall C-160 des deutschen ISAF Kontingents am Mittwoch (21.02.2007) in Afghanistan. Foto: Rainer Jensen +++(c) dpa - Report+++

d

Jiragen saman dai zasu tallafa ga yaƙin da sojojin ƙasar faransa da na nahiyar Afirka ke yi da yan tawayen Mali.A wani taron manema labarai da ministan tsaro na ƙasar ta Jamus thomas de Maiziere ya yi tare da ministan harkokin waje waɗanda sun ce jiragen zasu shiga hannu ƙungiyar ta ECOWAS nan bada daɗewa ba.

Yanzu haka manyan kwamandojin soja na ƙungiyar ta Ecowas na can na gudanar da taro a ƙasar Cote d'Ivoire domin tattauna maganar ta aikewa da dakarun yankin na yammacin Afirka zuwa Mali, a sa'ilin da faɗa ya rincaɓe tsakanin sojin Faransa da ke damafama dakarun gwamnatin da na yan tawayen a yankin arewacin Mali.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman