1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Deutsche Islamisten im Irak

June 17, 2014

Jamusawa da wasu Turawa na kasashen yamma suna tallafa wa mayakan ISIS na Iraki, a gwagwarmayar da suke yi da makamai don kafa shari'ar musulunci.

https://p.dw.com/p/1CJn4
Irak Freiwillige Armeedienst Kampf gegen Isis Terroristen
Hoto: Reuters

Ko da shi ke dai turawan ba su da horo yaki da ya dace, amma kuma hukumomin Jamus na nuna damuwa game da wannan batu, sakamakon kazancewa da rikicin ke yi tsakanin gwamnatin Iraki da 'yan ISIS.

Denis Cuspert wani mazaunin Berlin ne wanda a da aka sanshi da suna Deso Dogg a fagen salon kida da waka na zamani na Hip-Hop. Amma a yanzu ya na fafatawa a kasar Iraki a bangaren masu tsattsauran ra'ayin musulunci na Kungiyar ISIS, karkashin sunan Abu Talha al-Almani. Ya na daya daga cikin Jamusawan da suka rikide daga yada manufofin mazhabar Salafiyya i zuwa shiga yaki a Iraki da sunan yin Jihadi. Tsohon mawakin na Rap ne ma shugaban tsara salon yaki na Reshen Jamus na rundunar da aka fi sani da suna " Millatu Ibrahim", wanda mujallar "Focus" ta nunar da cewa babban mai shigar da kara na Jamus ya kudiri aniyar sa kafar wando guda da ita.

Su ma dai masu bincike na Spain sun bankado sirri wasu gungun 'Yan Kungiyar ISIS da suka nemi kutsawa kasar,domin neman wadanda za su fafata a kasashen Iraki da kuma Syriya. Ba yanzu ne dai Kungiyar da ke da tsattsauran ra'ayin addini ta fara neman cusa wa matasa na kasashen Turai da Amirka akidunta na kafa shari'ar musulunci ba. Ko da wani bincike da King's College na London ta gudanar, sai da aka gano cewar mutane dubu uku na kasashen yammacin duniya suke cikin kungiyar ta ISIS ciki kuwa da Jamusawa 320.

Irak ISIL Freiwillige
Mayakan sakai na IrakiHoto: Reuters

Falko Walde, kwararre a batutuwan da suka shafi Iraki a reshen Gidauniyar Friedrich Nauman da ke Amman na Jordan, ya bayyana dalilan matasan Turai na shiga cikin Kungiyar ISIS.

"Matasan mutane da ke sha'awar irin wannan akida. ISIS na daga cikin kungiyoyin da ke da tsattsauran ra'ayin addini da ke tafiye-tafiye daga wannan yanki i zuwa wancan domin yada manufofinta. Amma dai ta fi yin tasiri ne a kan matasa, musamman wadnda ke neman alkiblar da za su dosa."

Galibin Turawan da ke taimaka wa kungiyar ISIS sun musulunta ne. Sannan kuma suna bin mashabar Salafiyanci ne da ke ikirarin yada shika-shikan addini na hakika. Dukkaninsu dai na bari dogon gemu. Hakazalika galibinsu dai ba su yi karatun a zo a gani ba. Sannan kuma ba su girma cikin wadata ba. Michael Kiefer, kwararren a fannin shari'ar musulunci a jami'ar Osnabrück na nan Jamus, ya ce rashin ba su kulawa da ta dace ne, ke sa matasan rungumar kungiyoyi irinsu na ISIS.

"Akwai wani kyakkyawan misali da wadanda mutane ka basu: akwai a bangaren daya mutane masu kyawawan hali, bayin Allah. Yayin da a daya hannun kuma akwai mugaye makiya Allah. Anan dai babu wani zabi, illa son shiga yaki koko a'a?."

Irak ISIL Freiwillige
Mayakan ISISHoto: Reuters/Alaa Al-Marjani

Ba yanzu ne dai Jamusawa suka fara shiga yake-yake daban daban na duniya da suna yin Jihadi ba. Bayan harin 11 ga watan Satumba na 2001 a Amirka ma dai, hukumomin Jamus sun bayyana cewa 'yan kasar da dama sun nuna sha'awar taimaka wa masu tsaurin ra'ayin addini na Tchetcheniya domin yakar Rasha. Sai dai kuma adadin su Jamusawan ya karu, lokacin da suke je taimaka wa taliban a yankin Waziristan na kasar Afghanistan. A Kasar Syriya ma dai ba a bar Jamusawan a baya ba wajen taimakawa 'yan tawayen da ke neman hambarar da Bashar al-Assad.

Saboda haka ne ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere bai yi mamakin shiga Jamusawa yakin Iraki ba.

"Idan aka yi la'akari da cewa wannan kungiya ta ISIS ne ke fafatawa a Syriya, to kowa zai kwana da sanin cewa za a yi amfani da masu gaggwarmaya na Turai a yakin Iraki. Wannan kuwa abu ne da ke matukar tayar mana da hankali."

Sai dai kuma ministan bai bayyana takamaimen matakin da za a dauka a kan wadannan Jamusawan da ke suka shaga yakin Iraki ba.

Mawallafi: Mouhamadou Auwal Balarabe
Edita : Zainab Mohammed Abubakar