1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargi China da yiwa al'umma barazana

Zulaiha Abubakar
August 15, 2019

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci masu zanga-zanga da mahukunta a yankin Hong Kong su nemi hanyar warware rashin fahimtar juna da ke tsakaninsu cikin lumana.

https://p.dw.com/p/3NvaA
Angela Merkel Sommerpressekonferenz Berlin
Hoto: Reuters/H. Hanschke


Merkel ta kuma kara da cewar a baya yankin na Hong Kong ya yi fice wajen baiwa mazaunansa 'yancin bayyana ra'ayinsu, daga nan sai ta bayyana takaicin game da yadda rikici ya samu gurin zama tsakanin mazauna da mahukuntan yankin cikin takaitaccen lokaci.

Yanzu haka dai jami'an tsaron kasar China tare da manyan motocin yaki na atisaye a kudancin birnin Shenzhen cikin shirin yanki, lamarin da ya fusata mazauna Hong-Kong tare da janyowa gwamnatin China wacce ta tsuke bakinta game da wannan danbarwa Allah wadai daga bangarori da dama.