1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus na ƙoƙarin shiga tsakani a rikicin Gabas ta Tsakiya

August 11, 2013

Jagoran diplomasiya na ƙasar Guido Westerwelle ya isa a Isra'ila inda zai gana da shugabannin domin tattauna batun shirin wanzar da zaman lafiya a yankin.

https://p.dw.com/p/19Nfh
Wann: 3. u. 4.7.2013 Wo: Athen Anlass: Besuch von Außenminister Westerwelle Guido Westerwelle Ankunft Flughafen Athen
tHoto: Panagiotis Kouparanis

Guido Westerwelle zai gana da shugaba Shimon Peres da kuma babbar minista mai shiga tsakanin ta ƙasar Tzipi Livini, kafin a gobe Litinin ya sadu da Firaminista Benjamin Netanyahu da kuma shugaban Palastinawa Mahamud Abbas,domin tattauna batun sake farfaɗo da shirin zaman lafiya. Bayan shekaru uku da shirin ya cije a rikicin da aka kwashe sama da shekaru 60 ana yi tsakanin ƙasashen biyu.

A watan da ya gabata na Yuli masu sasantawa na ƙasar wato Saeb Erkat da Tzipi Livini suka sake komawa kan teburin shawarwari tare da shiga tsakanin na Amirka. Nan gaba a ranar Laraba mai zuwa ce za a soma gudanar da wasu sabbin shawarwari tsakanin Yahudawan da Palastinawa a biranen Jerusalem da kuma Jeriko da ke a yankin Zirin-Gaza.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Edita Yahouza Sadissou Madobi