1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hana bayar da kudade ga Masallatai a Jamus

Zulaiha Abubakar
December 29, 2018

Ma'aikatar harkokin kasashen wajen Jamus ta bukaci kasashen Saudiya da Qatar da Kuwait da wasu kasashen na Larabawa, su fara sanar da duk wata gudummawa da za su bai wa Masallatan kasarta kafin mika su.

https://p.dw.com/p/3Aksk
Sehitlik Moschee in Berlin
Hoto: Getty Images/C. Koall

Jamus din ta ce ta umarci hukumomin tsaron ciki da wajen kasar da su sanya ido kan shige da ficen kudade a kasar tare da bukatar kasashen na Larabawa su sanar da mahukuntan Taraiyar ta Jamus a duk lokacin da wa ta kungiyar addini ta bukaci taimako daga garesu. Wannan mataki dai ya samo asali ne a yayin da ministan harkokin cikin gidan kasar Horst Seehofer ya gabatar da jawabi a lokacin babban taron Addinin Musulunci da aka gudanar a watan Nuwamban wannan shekarar a Jamus din, inda ya nemi kasashen ketare su daina shiga harkokin gudanarwar Masallatai a Jamus.