Jamus: Hadarin jirgin kasa ya kashe mutane | Labarai | DW | 09.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: Hadarin jirgin kasa ya kashe mutane

Akalla mutane takwas ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon karon da wasu jiragen kasa biyu suka yi a kusa da garin Bad Aibling na jihar Bavaria da ke kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ce hadarin ya auku ne daidai lokacin da mutane suke tururuwa wajen tafiya aiki da sanyin safiyar yau Talata.

Masu aikin ceto suka ce baya ga wanda suka rasu, wasu mutanen da yawansu ya kai 150 sun jikkata inda wasunsu ke cikin hali rai kwakwai mutu kwakwai.

Tuni aka aike da jirage ceto masu saukar ungulu domin kwashe wanda ke cikin mawuyacin halin domin kaisu aisbiti don ceton ransu. Ya zuwa yanzu ba a tantance dalilin aukuwar hadarin ba.