Jamus: An kame wani da ake zargin dan IS ne | Labarai | DW | 25.09.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jamus: An kame wani da ake zargin dan IS ne

'Yan sanda a Jamus sun cafke wani mutum mai shekaru 22 da haihuwa wanda ake kyautata zaton cewar dan kungiyar IS ne.

Matashin wanda 'yan sanda suka kama a filin saukar jiragen sama na Dusseldorf  da ke a yankin arewa maso yammacin Jamus ya zo ne daga kasar Turkiyya, kuma hukumomin tsaro na zargin cewar mutumin na kan hanyarsa ta zuwa Siriya domin samun horo na sarafa makamai. Masu ruwa da tsaki a kan sha'anin  tsaro na Jamus na hasashen cewar kawo yanzu  kimanin mutane 800 ne suka fice daga  Jamus domin don yin yaki da masu jihadi ko dai a Siriya ko kuma Iraki.