1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus: An jikkata mutane bikin Karneval

Ahmed Salisu
February 24, 2020

'Yan sanda a birnin Volkmarsen da ke jihar Hesse a nan Jamus sun ce wani mutum ya afka da mota kan masu kallon bikin Karneval a yau har ma mutane da dama sun jikkata.

https://p.dw.com/p/3YLUK
Deutschland Auto fährt in Rosenmontagszug in Volkmarsen
Hoto: Reuters/E. Schulten

Mai magana da yawun 'yan sandan birnin ya ce yawan wanda suka jikkata din sun kai 30 kuma suna da yakin cewar wanda ya aikata hakan ya yi ne da gangan sai dai ya zuwa yanzu basu san dalilinsa na yin hakan ba.

Ma'aikatar cikin gida ta jihar ta Hesse da ita ma ta tabbatar da faruwa wannan lamari ta ce da gangan mutumin ya aikita wannan danyen aiki kuma hakan ba zai rasa nasa da siyasa ba sai dai ya zuwa yanzu ba wani tabbaci da suke da shi a kasa.

Wannan lamari dai ya wakana ne daidai lokacin da aka kai kololuwar bikin na Karneval a yau, bikin da aka saba yi duk yi duk shekara a wasu manyan biranen yammacin Jamus, kuma ana yi wa wannan rana ta yau lakabi da Rosenmontag.