Jam′iyyu za su kafa gwamnati a Denmak | Labarai | DW | 20.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyu za su kafa gwamnati a Denmak

Rasmussen ya ce za su fara tattaunawa da dukkan mambobin majalisa daga jam'iyyu uku masu rinjaye a zaɓen kasar da aka yi ranar Alhamis.

Dänemark Wahlen Lars Lökke Rasmussen und Frau vor Wahllokal in Kopenhagen

Lars Lökke Rasmussen da matarsa kafin zabe

Jam'iyyun siyasa a kasar Denmak sun fara wata tattaunawa a ranar Asabar ɗin nan wajen ganin sun kafa gwamnatin gambiza kwanaki biyu bayan da jam'iyyar Danish People's Party (DPP) mai adawa da kwararar baki ƙasar ta samu karfin zama jam'iyya ta biyu mafi ƙarfi a wannan ƙasa.

Lars Lokke Rasmussen na jam'iyyar Venstre party da zai zama sabon firaminista ya fara tuntuɓar abokan kawancen nasu tun a safiyar Asabar ɗin nan bayan jan hankalin sarauniya Margrethe ta biyu ,inda ta buƙaci su kafa gwamnati da za ta maye gurbin gwamnatin premier Helle Schmidt.Rasmussen ya ce za su fara tattaunawa da dukkan mambobin majalisa daga jam'iyyu uku masu rinjaye a zaɓen ƙasar da aka yi ranar Alhamis farawa da neman haɗin kan jam'iyyar DPP.