Jam′iyyar ′yan mazan jiya na kan hanyar samun nasara | Labarai | DW | 08.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar 'yan mazan jiya na kan hanyar samun nasara

Sakamakon farko na zaɓen 'yan majalisun dokoki na Birtaniya na nuna cewar jam'iyyar da ke mulki ta David Cameron na kan hanyar samun nasara.

Sakamakon farko na zaɓen 'yan majalisun dokokin da aka soma bayyanawa a Birtaniya na nuna cewar jam'iyyar Conservatives ta David Cameron ke a kan gaba da yawan ƙuri'u.Yayin da jam'iyyar 'yan adawa ta masu ra'ayin kawo sauyi ta Labour ta ke take mata baya.

Wata jam'iyyar kuma da ta taka rawa ita ce jam'iyyar masu kishin ƙasa ta yankin Scotland.Ya zuwa yanzu dai ba a da cikakkiyar masaniya dangane da abin da zai iya biyo baya ko, jam'iyyar ita ka dai tana iya kafa gwamnti ko kuma sai ta nemi goyon ayan waau jam'iyyun siyasar.