1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Republican ta karbe iko da majalisar wakilan Amirka.

Binta Aliyu Zurmi
November 17, 2022

Da dan karamin rinjaye, jam'iyyar adawa ta Republican ta karbe madafan ikon majalisar wakilan Amurka daga jam'iyya mai mulki ta Democrats.

https://p.dw.com/p/4Jdbt
USA | Kapitol und Repräsentantenhaus
Hoto: Anna Moneymaker/Getty Images

Jam'iyyar Republican ta samu kujeru 218 wanda kuma sune ake bukata na samun rinjaye a majalisar mai kujeru 435. Wannan nasara dai ka iya zama kadangaren bakin tulu ga shugaba Joe Biden wajen gudanar da wasu ayyukanshi a sauran shekaru biyu na wa'adin da ya rage mishi.

Sai dai har yanzu jam'iyyar Democrats ita ke rike da majalisar Dattawa. Wannan nasara ta jam'iyyar adawa na zuwa ne kwana guda bayan da tsohon shugaban kasar Donald Trump ya sanar da aniyarsa ta tsayawa takara a zaben shekarar 2024.

Tuni shugaba Joe Biden ya mika sakon taya murnarsa ga Kevin McCarty wanda yanzu haka ke shirin zama kakakin majalisar wakilai.