Jam′iyyar Labour ta yi sabon shugaba a Birtaniya | Labarai | DW | 12.09.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar Labour ta yi sabon shugaba a Birtaniya

Kasancewar Corbyn jagoran wannan jam'iyya ta Labour na zuwa ne bayan da ya samu kashi 59.5 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Jeremy Corbyn

Jeremy Corbyn jagoran Labour Party

Dan fafutika mai ra'ayin sauyi da ke adawa da shirin tsuke bakin aljihu a Birtaniya Jeremy Corbyn ya zama sabon jagora a jam'iyyar Labour Party da ke zama babbar jam'iyyar adawa a kasar Birtaniya. Kasancewarsa jagoran wannan jam'iyya ta Labour na zuwa ne bayan zaben da aka yi inda ya samu kashi 59.5 cikin dari. Jam'iyyar tasa ta bayyana wannan nasara a ranar Asabar din nan yayin wani taro na musamman da aka tsara.

Mista Corbyn dai ya bayyana bukatarsa ta ganin an samar da makoma ta gari ga Birtaniya. Corbyn ya yi nasara kan Andy Burnham da Yvette Cooper da Liz Kendall.