Jam′iyyar Ennahda na komawa baya a Tunisia | Labarai | DW | 27.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar Ennahda na komawa baya a Tunisia

Sakamakon farko a zaben 'yan majalisar dokokin kasar Tunisiya da aka yi jiya Lahadi, ya nuna jam'iyyar da ba ruwan ta da addini Nidaa Tounes, na ci gaba da samun karbuwa

Jam'iyyar da ba ruwan ta da addini Nidaa Tounes a kasar Tunisiya ta samu nasarar samun kujeru sama da 80 cikin zaben majalisar dokokin kasar da ke da kujeru 217, inda jam'iyyar masu ra'ayin Islama ta Ennahda ta samu kashi 67 na kujerun a cewar wasu majiyoyin jam'iyyun cikin sakamakon da ke fara fitowa.

A yau Litinin ne dai ake saran bayyanar baki dayan sakamakon daga hukumar da ke tsara zabe a kasar ta Tunisiya, idan har kuma ta tabbatar da wannan sakamako hakan na iya zama babban koma baya ga jamiyyar ta Ennahda wacce ta fi yawan kujeru a zaben shekarar 2011 bayan faduwar gwamnatin shugaba Zine el-Abidine Ben Ali.

Al'ummar kasar ta Tunisiya dai sun zabi sabbin mambobin majalisar dokokin kasar a jiya Lahadi a zaben da ke kara sanya wannan kasa rungumar dimokradiya tun bayan kifar da gwamnatin Ben Ali da ta zama sila ta juyin-juya hali da aka samu a tsakanin kasashen Larabawa.

Ganin babu wata jamiyya da ake kallon za ta kwashe mafi yawan kujerun, akwai yuwuwar samun jamiyyun hadaka makonni da ke tafe.

Mawallafi: Yusuf Bala
Edita: Suleiman Babayo