Jam′iyyar da ke mulkin Siri Lanka ta samu nasara | Labarai | DW | 18.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar da ke mulkin Siri Lanka ta samu nasara

Masu zabe a Siri Lanka sun dakile yunkurin tsohon shugaban kasar na sake dawowa mulki a matsayin firaminista inda jam'iyya mai mulki ta samu nasara a zaben 'yan majalisa

Jam'iyya mai mulkin kasar Siri Lanka karkashin Firaminista Ranil Wickremesinghe ta lashe zaben 'yan majalisar dokokin kasar, inda ta samu kujeru 106, yayin da jam'iyyar tsohon Shugaba Mahinda Rajapaksa ta samu kujerun majalisa 95, daga cikin kujeru 225 da majalisar ta kunsa. Haka ya kawo karshen yunkurin tsohon Shugaba Rajapaksa na sake dawowa mulkin kasar a matsayin firaminista.

Kimanin kashi 70 cikin 100 na masu zaben milyan 15 sun kada kuri'a, yayin zaben na jiya Litinin. Sai dai duk da nasarar Firaminista Ranil Wickremesinghe na kasar ta Siri Lanka yana bukatar goyon baya daga kananan jam'iyyu domin samun 'yan majalisa 113, kafin ya sake kafa gwamnati karkashin Shugaba Maithripala Sirisena, wanda ya doke tsohon Shugaba Mahinda Rajapaksa lokacin zaben watan Janairu.