Jam′iyyar ANC na shirye-shiryen zaɓe | Labarai | DW | 04.05.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Jam'iyyar ANC na shirye-shiryen zaɓe

Fiye da mutane dubu ɗari ne suka halarci wani taron da jam'iyyar ta kira a Filin ƙwallon ƙafa na Soccer City na Soweto.

Jam'iyyar mai mulki ta ANC a Afirka ta Kudu, ta gudanar da wani gaggarumin taron gangami a yau Lahadi (04.05.2014) a birnin Saweto, inda a ƙalla mutane dubu 100 suka halara, yayin da kwanaki uku kacal ne suka rage a gudanar da zaɓen 'yan majalisun dokoki.

Abin da ke nuna cewar magoya bayan jam'iyyar sun share duk wani zargin cin hanci da aka yi wa shugaban ƙasar Jakob Zuma a yayin yaƙin neman zaɓen da ya gudana a faɗin kasar.Tuni dai da binciken jin ra'ayoyin Jama'a ya nunar da cewar, a ƙalla fiye da kishi 60 cikin ɗari ne na 'yan ƙasar ke son goyon bayan jam'iyyar ta Nelson Mandela a zaɓen.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane