Jam′iyyar ANC na gudanar da taro | Siyasa | DW | 30.06.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Jam'iyyar ANC na gudanar da taro

A Juma'a ce jam'iyyar ANC da ke mulki a Afirka ta Kudu ta fara gudanar da wani taro na kwanaki biyar wanda a ake sa ran za ta dau matakan kawo karshen irin rikicin cikin gidan da jam'iyyar ke fuskanta.

Zargi na cin hanci da rashin aikin yi da kuma karancin aiyyukan raya kasa na daga cikin irin abubuwan da suka sanya wasu 'yan Afirka ta Kudu yanke kauna da jam'iyyar ANC da ke mulkin kasar. Wadannan matsaloli ma dai na daga cikin irin abubuwan da jam'iyyun da ke adawa da ANC ke dauka a matsayin dalilai na ganin an kawar da ita daga gadon mulki a zaben gama-gari na gaba da 'yan kasar za su gudanar. To sai dai a daura da wannan, jam'iyyar ta tashi haikan wajen ganin ta samo bakin zaren wadannan matsaloli musamman ma dai matsin lambar da ta ke sha daga 'yan adawa na ganin an tsige shugaban kasar Jacob Zuma daga gadon mulki saboda da abin da suka kira gaza tabuka komai da kuma irin yadda shugaban ke keta doka. ANC din dai na son amfani da taron wajen bijiro da sabbin dabarun da za a yi amfani da su wajen daidaita lamuran ta. A share guda kuma jam'iyyar na fuskantar matsala ta rarrabuwar kawuna tsakanin mambobin ta don tuni ma masana harkokin siyasa irin su Theo Venter na jami'ar North West da ke kasar ya ce jam'iyyar za ta iya fuskanta babban koma baya a zabuka na gama-gari da za a gudanar a kasar a shekaru biyun da ke tafe.

 

Sauti da bidiyo akan labarin