Shugaba Ramaphosa na fuskantar zargi
October 10, 2018Ajiye aikin ministan kudin ya biyo bayan sanarwar ganawarsa da iyalan Gupta wadanda ake zargi da satar kudaden kasar a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Jacob Zuma.Yayin da yake rattaba hannu kan bukatar ajiye aikin ministan shugaban kasar ya jaddada wa al'ummar kasar aniyarsa ta yakar cin hanci lamarin da ya janyo wa tattalin arzikin kasar karewa , 'yan jam'iyyar adawa dai na ci gaba da kiraye-kirayen sai shugaba Ramaphosa ya bayyana wa al'ummar kasar bayanan da yake da su a game da karkatar da kudaden gwamnatin da yayi sanadiyyar saukar tsohon shugaban kasar daga kujerar mulki.
Tuni fadar shugaban kasar ta sanar da Titö Mboweni tsohon shugaban bankin kasar a matsayin sabon ministan kudin kasar lamarin da 'yan adawa suka yi Allah wadai da shi.