Jami′yayar ANC ta umarci Zuma ya yi murabus | Duka rahotanni | DW | 13.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Duka rahotanni

Jami'yayar ANC ta umarci Zuma ya yi murabus

Tun bayan da jam'iyyar ANC mai mulki a kasar Afirka ta Kudu ta sanar da daukar matakin sauke shugaba Jacob Zuma daga mukaminsa jama'a suka soma baiyana ra’ayoyi mababanta kan batun,

Duk da cewa wannan ba shi ne karon farko da shugaba Jacob Zuma ke fuskantar matsi na ganin ya sauka daga mulkin kasar ba bisa badakalar cin hanci da kuma yin sama da fadi da dukiyar kasa ba, amma ganin matakin da kwamitin gudanarwar jam’iyyarsa ya zartar bayan share tsawon lokaci ana ganawa ya sa ake ganin watakila lokaci ya yi da shugaban da ya dare mulki a shekarar 2009 zai amsa wannan kiran ya sauka

Sanarwar jam’iyyar dai na cewa Zuma ya amince da yin murabus amma ya nemi a ba shi damar ya ci gaba da jan ragamar mulki na ‘yan watanni kafin cikar wa’adin mulkinsa, sai dai ya’yan jam’iyyar ta ANC sun yi fatali wannan bukata kamar yadda babban sakataren jam’iyyar Ace Magashule ya sanar.

Südafrika Zuma hält Rede im Orlando Stadion in Soweto (Getty Images/AFP/M. Safodien)

Taron 'yan Jam'iyyar ANC a Airka ta Kudu

''Duk da cewa mun mutunta bukatar shugaba Zuma kan batun sauka daga mulki, kwamitin gudanarwa ya gano Afrika ta kudu na cikin wani hali na matsi a dalilin wannan badakala ta meka mulki, don haka kwamitin na ganin akwai bukatar daukar matakin da ya dace don fitar da kasa daga cikin wannan kangi a kokarin hada kan kasa dama fatan ciyar da kasar gaba.''

Ga sauran al’umma da suka dadde suna kallon dambarwar siyasar kasar ta Afrika ta Kudu kuwa, sun ci gaba da tofa albarkacin bakinsu, inda mafi yawa ke ganin yanzu lokaci ya yi da ya kamata shugaban ya yadda kwallon Mangwaro domin ya huta da kuda a cewar wata 'yar kasar Kebolokile Morobisi.

Südafrika ANC Parteitag Zuma und Ramaphosa (picture-alliance/AP Photo/T. Hadebe)

Zuma da wanda zai gaje shi Cyril Ramaphosa

" A gaskiya mun gaji da wannan badakala na cin hanci da rashawa a kasarmu, kuma ina ganin saukar shugaba Zuma daga mulki zai taimaka mana matuka wajen ciyar da kasarmu gaba. Lokaci ya yi da zai koma gefe guda, domin ya jagoranci kasarmu na tsawon shekaru 9. Don haka Baba zuma lokaci ya yi ka sauka, ka huta kamar Mugabe a Zimbabwe".

A daya bangaren kuwa akwai wadanda ke kallon wannan lamari na tilastawa shugaban wanda ya taka mahinmiyar a fafutukar yaki da mulkin wariya a kasar ta Afrika ta kudu a matsayin wata bita da kulli a fagen siyasa.

 

 

 

Sauti da bidiyo akan labarin